Monday, January 11, 2016

JAWABIN BUDEWA

Jama'a Assalamu Alaikum. Ina yi muku maraba lale zuwa wannan sabon shafi da na bude domin samar da bayanai akan nazarin Hausa da Hausawa da kuma masana masu nazarin harshen Hausa da adabinsu da al'adunsa. Burin wannan shafi ne ya gabatar da sunayen manazartan Hausa da suke a jami'o'in Nijeriya da sauran kasashen, da wadanda suke manyan makarantun gaba da sakandare da ma masu zaman kansu. Za mu yi kokarin samar da bayanai da za su taimaki manazarta da dalibai da ma duk wani mai sha'awa akan harshen Hausa da Hausawa. Muna fatan samun hadin kan jama'a ta hayra taimaka mana ta duk hanyoyin da suka dace. Allah ya sa mu dace amin.

1 comment: